KALAMAN SODA KAUNA ZALLA DON MASOYA KADAI - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Wednesday, May 16, 2018

KALAMAN SODA KAUNA ZALLA DON MASOYA KADAI

Zuciyarki ta zama takarda, tawata zamabiro
in rubata miki shafin kauna Kizama kofa na
zamao makulli, mu hadu mubude kofar
soyyar lambun
zuciyata Na kasa tsaye na kasa zaune a
lokacin da na fara ganin ki a cikin taro , kin
fita daban kaman wata a daren sha biyar
Watau yau
da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske
garin nan, amma duk hasken ta ba kai
hasken fuskar da haske zuciyata,domin ni a
zuciyata Hasken fuskar abun quana ta yafi
duk hasken raina Ki zama petur na zama inji
mu hadu mu ta da lantarkin qauna ya shiba
ta na baki filin zuciya ta ki shuka a duk wani
lungun da sako bushiyar so a kauna don mu
sami inuwar da zamu zauna muyi soyayya.

Kece madubi abar dubawata duk safiya, kin
zamo min tamkar fetur a mota, rayuwata ba
ke lami ce ya rabin raina.Ke ce
makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na
sha za ta haskaka zuciyata tayi fari.
Rayuwata babu ke tamkar wayar da ba
wayar chaji ce, kuma babu layi, a mace ba
amfani.

Kunne ya kurmance saboda
rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya
daina magana dai dai saboda rashin begen
zumar rayuwata kullum. ya tsagwaron zallar
tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona zai
makance saboda rashin
ganinki a yau da kullum Ya gangariyar
madarar zumar da bata da gauraye, ya
tauraruwa a cikin
jinsin taurari mai haske zuciyar masoyinta.
Idona ya bude ya ga haske irin na walkiya
don ya gan ki.

Zuciyata na shan lawgadar zuma da madarar
kauna Idon basira lafazin
rayuwata Alfijir na qauna ya keto,
tsuntsayen soyayya sun tashi su na yayo a
sararin Samantha tzu citata
Ya fankar da ke juya zuciyata, zan zamo
kwale kwale ki shigo mu hau kan kogin so, in
zamo katifa ki zamo gado a cikin dakin
kauna. Hadarin begen ki ya hado, guguwar
sonki
ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi
na kaunar ki a filin zuciyata. Gaisuwa daga
kamfanin so, harabar kauna,
gida mai lambar zuciyata layin begen ki,
zuwa ga rabin rayuwata. ya zare da allurar
da ta dinken
zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai
wutarlantarki ta zauna a nijeriya ya
majaujawar zuciya ta, zan
zama guga ki zama igiya mu hadu a jefa mu
cikin rijiyar soyayya.

Ya tsokar zuciya ta, zan
so ace ki zama fura in zama nono mu hadu
a
kwaryar soyayya. Ya sahiba ta ki zama
fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu
ta da tsuntsun soyayya.

Ya masoyiyata, ki
zamo bishiya in zamo ruwan da zai ratsa ta
kasar so ba dan kome ba sai dan in shayar
da ke domin samun kalaman soyayya kawai
ka kasan damu ako yaushe a wannan shafin
www.hausanet.ml domin samun zafafan
kalamai

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad