*💌KUNDIN MA'AURATA //08💞*
*_SHASHANTAR DA MAGANA_*
Daya daga cikin abubuwan da suke baqanta wa mace rai shi ne lokacin da za ta riqa jin an mai da ita kamar saniyar ware a kan abin da take jin cewa tana da rinjaye, misali diyarta da take auren wani yaro dan kasuwa, tana jin cewa ana cutar mata da yarinyar gwargwadon yadda bincikenta ya nuna a wurin yarinyar, tabbas za ta iya gasgata yarinyarta saboda abu biyu, na farko dai ita ta raini yarinyarta ta san halinta, na biyu kuma duk alamomin damuwa da rashin jin dadi suna bayyana a fuskarta da jikinta, don haka ta yi wa mijinta, wato uban yarinyar, maganar cewa ya je ya binciko abin dake faruwa, ta fahimci cewa yaronnan so yake ya yi wa diyarsu yankar qauna, da maigidan ya dawo matarsa tana zaton zai yi mata magana bai ce komai ba, shi ya sa ta qyale shi har zuwa lokacin cin abincin darensa, sannan ranta ma ya gama baci.
Yana dab da kammalawa ta tambaye shi ko zai sha shayi, ya ce bai da buqata, sai ta ce "Ina zaton za ka gaya min yadda kuka qare da wancan yaron ba ka ce komai ba! Ka gan shi kuwa" ya ce "I na gan shi, kuma mun dan tattauna na tsawon lokaci" a maimakon ya yi mata bayani sai ya yi shuru, qila shi yana ganin cewa lamarin abu ne da ya shafi maza zalla, ita kuma ba abin da ya fi mata zancen diyarta, za ta so ta ji yadda lamarin ya kaya, ta ce "Ban gane kun tattauna ba, wai me ke faruwa ne?" Ya ce "Mts! Wasu 'yan abubuwa ne qanana, in da za su zauna su tattauna ba ma sai wani ya shiga tsakaninsu ba"
Shi yana sauqaqa abin ne yadda mahaifiyar ba za ta shiga cikin maganar ta tada zaune tsaye ba, a ganinsa ya riga ya magance matsalar, ta ce "To ai kai ba haka ake yi ba" tana qoqarin ta san hanyar da ya bi ne wurin magance matsalar "Kamata ya yi ka tara su a gabanka, ka ji ta bakin kowa, ba ka kira shi shi kadai ka saurare shi ba" anan ransa zai baci, saboda tunanin cewa ta raina hankalinsa, don ita ce ma take qoqarin gaya masa me ya kamata ya yi, in ba sa'a aka yi ba sai ya bar asalin maganar da suke yi, wace inda zai ce haka na yi shi kenan ya gama, amma sai ya kama ta da fada "Wai ke me yasa ba ki da haquri ne? In kina ganin kin fi ni sanin yadda za a daidaita su bismillah! Sai ki je ki tanqwara shi ya tafiyar da yarinyarki yadda kike so" a wannan misalin ma an sami sabani, wanda zahirinsa shurun namijin ya kawo shi, mace tana son a kawo mata komai a fassale, tana son a riqa tattaunawa da ita, namiji kuma bai cika son lugwigwita magana ba.
Ba fa dole ya zamto 'yarsu ce da gaskiya ba, kamar yadda zai iya kasancewa mijin 'yar yake da gaskiyar, a duk biyun uban yarinyar yana ganin za su iya daidaita kansu masamman yadda ya ja kunnensu dukansu, ya kuma nuna musu hatsarin kasantuwarsu a irin wannan yanayin na rashin fahimtar juna, tunda sun nuna sun ji abin da ya ce shi kenan magana ta qare, ita kuma uwar ba ta san hanyar da aka bi ba, ta san maza da rashin kula halin diyoyinsu mata, sai a yi ta cutar da su ba tare da sun nuna kulawarsu ba.
Akwai misaloli da dama wadanda maza sau tari ba sa sakin jiki da matansu su yi musu bayani, a qarshe kuma in abin bai yi kyau ba macen ita ce abar zargi, misali "Baqina za su zo ki tabbatar an gama komai kafin lokacin" ta amsa "In sha Allah, amma ka kawo kayan hadin da wuri, mutum nawa kake jin za su zo?" Ya ce "Ban sani ba, amma ki yi yadda zai isa" "Kana ganin za su kai 10-15?" "Na ce miki ban sani ba, ki yi yadda zai isa kawai, kar kuma a banzatar da abinci, ba wanda bai san halin da ake ciki a yau ba".
Nan ma a dunqule aka ba ta ba tare da bayani ba, in bai kai ba a ce ta yi qoro, in ya rage kuma a ce ta yi almubazziranci, rashin yi wa mata magana yakan dagula abubuwa da daman gaske, koda yake wani sa'in suna da zaulaya, ba abin da suke nufi kenan ba, amma maigidan sai ya fusata, misali za su yi baqi ne, kuma 'yar shinkafar da suke ci ta kusa qarewa, qila da safe ma sun tattauna qarewar tata da rashin kudin sayo wata, dan sauran duk ba ta wuce mudu 6 ba, kenan ba za ta kai su kwana 10 ba za ta qare, lokacin da ya yi maganar dafa wa baqi abinci sai ta ce "Kamar mudu nawa zai isa, kana ganin 7 ya yi?"
Tana sane ko ta gidan ba ta kai 7 din ba, in haushi ya cika shi sai ya gaya mata magana, ko ya jefa mata kudin hannunsa ya yi waje, ba tare da ya gaya mata yadda za a yi ba, kamata ya yi ta gama sauraronsa tukun, in ma zaulayar za ta yi sai ta yi masa a qarshe, kamar kuma lokacin da suka gama tattauna matsalar gida, da rashin kudi, ga kayan abinci duk sun qare, a qarshe-qarshen hirar sai ta dauko wata magana "Ni da ma za ka dan biya ni bashin da nake binka da na ji dadi, ga shi ma salla ta matso, wallahi ban da ko sisi a dakinnan, dan jarin da nake dan juyawa ma duk ka gama amshewa, don Allah zan dan sami ko rabi ne albashi sauran in ka samu sai ka cika min?"
Shi ma wannan in ba sa'ar aka ci ba zai iya zama laifi, don kuwa da ita aka tattauna rashin kudinnan amma ta juya baya kamar ba ta san komai ba, sai ka ga maigida ya yi kinini da fuska ya bata rai ya qi cewa komai, ko ta yi masa magana kuma ba zai ba ta amsa ba, wannan zai sa ko ta canja batun ba dole ba ne ya sake tanka mata, ba wai don ta yi masa maganar kudi ba, a tunaninsa baqanta masa rai take son yi, mun yarda maza suna da saurin fushi, kuma sun dauki hanyar qin yi wa mace magana ita ce zababbiyar hanyar da za su huce fushinsu, ko kuma su nuna mata cewa ba su ji dadi ba, wanda hakan a wajen mace kuskure ne, sau da yawa ba ta ba wa abu mahimmanci, namiji kuma yakan dauke shi da zafi, to amma ita ma ya dace ta riqa zaben lokutan da za ta yi wasa da lokutan da take kallon abubuwa a haqiqaninsu.
Zamu ci gaba insha Allah.
Rubutawa: Baban Manar.
Gabatarwa: Abu-Unaisa.
Wallafawa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
No comments:
Post a Comment