Tsohon Gwmanan jihar Kano kuma jigo a
jam'iyyar PDP Malam Ibrahim Shekarau ya ce
zai yi farin ciki idan Sanata Rabiu Musa
Kwankwaso ya koma PDP daga jam'iyyar APC.
Ana rade-radin cewa jagoran na
Kwankwasiyya zai iya barin jam'iyyar APC
bayan da uwar jam'iyyar ta goyi bayan
Gwamna Abdullahi Ganduje a rikicin
shugabancin da suke yi.
Hakazalika kuma ana ganin yana sha'awar
yin takarar shugabancin kasar a zaben 2019,
sai dai bai fito ya bayyana hakan ba kawo
yanzu.
Sai dai Malam Shekarau, wanda shi ma ke
son yin takarar shugabancin kasar a PDP, ya
shaida wa BBC cewa kawo yanzu babu wata
magana tsakaninsa da Kwankwaso kan shirin
komawarsa PDP.
An dade ana rashin jituwa a siyasance
tsakanin Malam Ibrahim Shekarau da Sanata
Rabiu Musa Kwankwaso, wadanda duka
manyan 'yan siyasa ne a Najeriya.
Ya ce ko a baya ma, ba shi da wata matsala
tsakaninsa da Kwankwaso, kuma ba shigar
Kwankwaso APC ce ta sa ya fita ba.
Duka mutanen biyu sun mulki jihar Kano
tsawon shekara takwas-takwas, kuma suna da
dimbin magoya baya.
Kuma wasu na ganin hadewarsu wuri guda za
ta bai wa jam'iyyar APC gagarumar matsala
ba wai a Kano ba nhar ma da wasu sassan
kasar.
No comments:
Post a Comment