An gano cewa maganin da ake bai wa masu ciwon kashi da ake kira osteoprosis zai iya samar da waraka ga masu sanko - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Thursday, May 10, 2018

An gano cewa maganin da ake bai wa masu ciwon kashi da ake kira osteoprosis zai iya samar da waraka ga masu sanko

An gano cewa maganin da ake bai wa
masu ciwon kashi da ake kira osteoprosis
zai iya samar da waraka ga masu sanko.
Masu binciken sun ce sun gano cewa
maganin yana tasiri a ramin gashi a
gwajin da suka yi, inda yake sa gashi ya
tsiro.
Yana kunshe da wani sinadari da ke dakile
tasirin sindarin Protein da ke sa gashi ya
zube da haifar da sanko.
Jagoran ma su binciken Dakta Nathan
Hawkshaw ya shaidawa BBC cewa za a yi
gwaji domin a tabbatar da maganin ba shi
da illa ga mutane.
A yanzu magunguna biyu ne kawai ake da
su na masu sanko:
1. Maganin minoxidil, na mata da maza.
2. Maganin finasteride, na maza kawai.
Sai dai dukkaninsu na yin illa a jikin
bil'adama, shi ya sa a mafi yawan lokuta
masu sanko ke zuwa asibiti domin yi mu
su dashen gashi.
Binciken da aka wallafa a Mujjalar PLOS
Biology an yi shi ne a cikin wani dakin
gwaji inda aka yi amfani da samfuri da ke
dauke da gashin wasu maza su fiye da
arba'in wadanda aka yi wa dashen gashi.
Masu binciken daga jami'ar Manchester,
sun fara aiki ne kan wani sindari da ake
kira cyclosporine A, wanda aka yi da shi
tun daga shekarun 1980 a kan marasa
lafiya da aka yi wa dashen koda ko hanta
da saraunsu.
Masana kimiyar sun gano cewa maganin
na rage tasirin sinadarin protein da ake
kira SFRP1, wanda yake da muhimmanci
wajan ragewa da kara tsawon gashi.

Sai dai saboda illar CsA ba za a iya amfani
da shi ba akan ma su sanko.
Masu binciken sun sake yin nazari kan
wani sinadari da ake kira WAY-316606
kuma sun gno cewa yana tasiri sosai wajan
rage kaifin sinadarin protein.
Dakta Hawkshaw ya ce maganin zai iya
sauya rayuwar mutane "ma su sanko" .

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad