Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Friday, May 11, 2018

Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu


A ranar Alhamis dinnan ne wata babbar
kotu a kasar Sudan ta yankewa wata
yarinya 'yar shekara 19 hukuncin daurin
rai da rai, sakamakon kashe mijinta da
tayi domin yayi mata fyade.

Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar
Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take
gaya wa kotu
A ranar Alhamis dinnan ne wata babbar
kotu a kasar Sudan ta yankewa wata
yarinya 'yar shekara 19 hukuncin daurin
rai da rai, sakamakon kashe mijinta da
tayi domin yayi mata fyade. Anyi kira ga
shugaban kasar ta Sudan Omar Al-Bashir
da yayi mata rangwame domin kuwa anyi
mata auren dole ne kuma da yarinta a
tattare da ita.

Sannan kuma tayi hakan ne
don ta kare mutuncin kanta

Noura Hussain tace, mahaifinta shine ya
tilasta mata auren Dan uwanta lokacin da
take shekaru 16.

Inda ta gudu, ta koma
zama tare da wasu danginta na tsawon
shekaru uku.

Ta koma gidan iyayenta da yake Khartoum
ne a watan Afirilu bayan mahaifin nata
yace an fasa auren,inda daga baya ta gane
wayau aka mata domin kuwa ana ta shirin
bikin ta bata sani ba.

Hussein tace ta hana mijinta kanta bayan
auren, amma a kwana na shida yayi mata
fyade bayan da 'yan uwanshi uku suka
ririke ta.

Washegari, ya je kara mata fyade ne, tayi
kokarin hanashi ta hanyar soka mishi
wuka, inda ta kashe shi har lahira.

Wata kotun shari'ar musulunci ta kama
Hussein da laifin kisan ganganci.

An ba lauyan ta damar daukaka kara a
cikin kwanaki 15.

"A bisa ga Shari'ar musulunci, dangin mijin
zasu iya karbar diyya ko kuma kotu ta
hukunta ta ta hanyar kisa.

Dangin shi kuwa
sun zabi kisa akan diyya.

" inji Badr Eldin
Salah, wani lauya mai kare hakkin bil
adama na Nahiyar Afirka wanda yake
kotun ranar da akayi shari'ar.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad