YAUSHE ALI DA ZANGO ZA SU DAINA GABA? - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Thursday, May 17, 2018

YAUSHE ALI DA ZANGO ZA SU DAINA GABA?

Koda yake, na ɗan kwana biyu ban yi
magana game da gabar da ta ke tsakanin
fitattun jaruman Finafinan Hausa ba
wato, Ali Nuhu da Adam A. Zango.

Ba ku ma so na ke na tsokano gabar ta
dawo farko ba. Sai dai waɗannan
jaruman ku san duniya ta shaida cewa
basu magana da junan su, tun bayan
wani saɓani da ya shiga tsakanin su a
watan Disamba na shekarar da ta
gabata, wanda abin kunya ne a ce har
yanzu basu daidaita ba a matsayin su na
'yan uwa musulmai. Shin wai ko dai
basu san illar da ke tattare da waɗanɗa
suke gaba da junan su ba? Ko kuma sun
sani suka take sani? Ko suna sane sai
sun je wajen Allah sai ya yi masu
hukuncin daidai da abin da suka aikata
a duniya.

Wadansu bangaren na jaruman da
magoya bayan su, sun ɗauki wani tsarin
rayuwa na daban marar dadi wanda ya
sha bamban da irin rayuwar da
Alƙur'ani ya nuna. Daya daga cikin
kurakuran da irin wadannan mutane
masu raunin imani da alfahari,
wadanda ba su damu da aikin yaɗa
sakon musulunci ta hanyar dabi’u masu
kyau ba, shi ne yadda suka dauki
rayuwar wannan duniya kawai ba ta
wuce mutum ya yi fim, ya samu ƙuɗi, ya
yi aure, ya haifi ‘ya’ya ya rene su
sannan ya tara abin duniya.

Amma inda kuskuren yake shine sun
manta da babban dalilin zuwansu
wannan duniya, da kin tafiyar da
ni’imomin da Allah ya yi masu na fifita
su da ya yi kan kowa a cikin
masana'antar da suke samun na wake da
shinkafa. Sun manta kwata-kwata suna
so duniya ta ruɗesu daga ƙarshe kuma
idan ba su sake ba dukkan su mota tana
iya aje su a tasha kamar yadda ta ɗauko
su.

Muna kira gare ku a matsayin ku na
'yan uwan mu musulmai “Ku bi Allah da
Manzonsa kuma kada ku yi jayayya a
junanku sai ku tarwatse karfinku ya tafi.
Ku yi hakuri. Allah yana tare da masu
hakuri.” (Suratul Anfal, aya ta 46)
Manzon Allah (S.A.W) ya ce Mutum biyu
sallar su bai wuce kawunan su. Na farƙo
nashayin giya, na biyu masu gaba da
junan su. A wani hadisin Manzon Allah
ya ƙara da cewa ana bude ƙofofin
aljanna ranar alhamis da litanin. Amma
an jinkirtawa mutum biyu sai sun
shirya (su ne Masu gaba da junan su)
Mun yi tunanin gabar taku ba mai
daɗewa bace, sai ga shi har watan azumi
yana shirin kamawa, amma ba ku shirin
yafewa juna.
Sources :kwannywoodexclusive

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad