Adamu Zango ya tayar da kura a Instagram - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Friday, May 11, 2018

Adamu Zango ya tayar da kura a Instagram

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan
Hausa, Adamu Abdullahi Zango ya tayar da
kura bayan ya sanya wadansu hotuna biyu a
shafinsa na Instagram.

Jarumin wanda ake kira da Fresh Prince ya
sanya hoto na farko hannunsa a kan kafadar
wata budurwa da ya kira ta da suna Hanaan.

A hoton jarumin da budurwar suna dariyar
farin ciki, sannan a karkashin hoton jarumin
ya rubuta kamar haka: “Yawancin mutane
suna so ku yi tafiya da su a cikin mota kirar
Limo, amma abin da kake so shi ne ka samu
wanda zai yi tafiya da kai a mota bas idan
Limo din ta baci.

Na yi farin ciki da ganin ki
@hanaan, ’yar uwata.”

Hoton ya tayar da kura, inda hakan ya sanya
jarumin ya kara sanya wani hoto mai dauke
da mutane hudu.

A hoto na biyun, jarumin ya dora hannuwansa
biyu a kan kafadun wadansu mata biyu, yayin
da wani matashi mai gemu yake daga farko ta
bangaren dama a hoton.

A hoton dukkansu
suna dariya.

Hakan ya sa wani daga cikin mabayan
jarumin a Instagram mai suna Hamid Ibrahim
cewa, “Wannan ba dabi’a mai kyau ba ce, a
dai rika yi ana tunawa da mutuwa.”
Ita kuwa Khadijat Arabi cewa ta yi sai masu
hassada da Zango su kashe kansu, amma
babu yadda za su yi da Zango.
“Sai dai masu hassada ku kashe kanku, amma
Zango ya yi gaba.” Inji ta.

Samira Hassan kuwa cewa ta yi, budurwar da
jarumin ya dora hannu a kafadarta yayin
daukar hoton, to ’yar uwarsa ce ta jini, don
haka babu wani laifi, ko abin cece-kuce da za
a ce jarumin ya jawo.

Shi kuwa Ahmed Isa cewa ya yi Zango abin
koyi ne ga miliyoyin jama’a, don haka bai
kamata ya rika sanya irin wadannan hotuna
ba.

Ya ce, “Zango kai babban jarumi ne, wanda
miliyoyin jama’a suke koyi da kai, don haka
bai kamata ka sanya irin wadannan hotuna
ba.”

Haka ne ya sanya Adam A. Zango yin karin
bayani, inda ya ce wacce ya dauki hoton da
ita kanwarsa ce, kuma babu laifi don ya taba
kanwarsa, al’amarin da ya sanya mutane suka
sake yi masa caa! Kasuwar kuda.
Ibrahim Idris ya ce, bai gamsu da bayanin da
jarumin ya yi ba, inda ya ba shi shawara ko
da zai dauki hotuna da ’yan uwansa, to ba
lallai sai ya dafa su ko ya rungume su ba.

“Koda ’yan uwansa ne bai kamata ya dafa su
ba, bai kamata ya rungume su ba, kowa ya
san yadda akuyar ’yan fim ta yi kuka, ana yi
musu kudin goro wajen kiransu ’yan iska, don
haka sai ya bar halal don kunya.

Ma’ana bai
san adadin wuraren da hotunan za su zaga
ba, ba kuma kowa ne zai gane cewa ’yan
uwansa ba ne, wadansu za su yi amfani da
hotunan wajen yada sharri.

“Su rika cewa ga abin da ’yan fim din Hausa
suke yi, kamar yadda aka rika yada na Nafisa
Abdullahi da Zainab Indomie da Ibrahim
Maishinku da sauransu, don haka ina ganin
rashin sanya hotunan shi ne mafi alheri a kan
sanya shi.” Inji Idris.

Amina A. Baba a lokacin da take tofa
albarkacin bakinta cewa ta yi ko da jarumin
zai sanya hotunan da suka shafi ’yan uwansa
ba lallai ne sai ya dafa su ba.

“Idan har ya zama dole sai jarumin ya sanya
hotunansa tare da ’yan uwansa, to bai zama
dole sai ya dafa su ba, za su tsaya ko su
zauna a dauki hoton ba tare da ya dafa su ba,
hakan kwata-kwata bai dace ba, kuma ya
kamata Zango ya sani shi fa ba yaro ba ne,
kuma ya san dole jama’a za su caccake shi
amma ya sanya, inda hakan yake nuna cewa
da gangan ya yi,” Inji ta.

Hakan ne ya sa daga baya jarumin ya boye
maganganun mutane dangane da hotunan,
duk da cewa har zuwa lokacin da aka
kammala rubuta wannan rahoto bai cire
hotunan ba.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad