Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Tuesday, May 8, 2018

Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta dawo da kudaden Abacha ya karkatar

- Kasar Amurka ta fadawa shugaba
Buhari cewa ba za ta amince da wasu
masu shiga tsakani ba wajen maido da
kudin Abacha ya ajiye a kasar

An gano kudaden ne tun zamanin
mulkin tsohon shugaban kasa,

Goodluck
Jonathan amma aka ajiye su a kasar
Amurka

- Ministan kudi, Kemi Adeosun ta
tabbatar wa 'yan Najeriya cewa dalla
miliyan 322.51 da zaka karba zai tafi
asusun tallafawa al'umma Najeriya ne
Gwamnatin kasar Amurka ta ce ba zatayi
hulda da wasu dillalai ba sai dai
gwamnatin Najeriya kawai wajen tattauna
yadda za'a dawo da dallan Amurka
miliyan 500 da tsohon shugaban mulkin
Soja, Sani Abacha ya ajiye a kasashen
ketare.

Amurka ta gindaya wasu ka'idoji kafin ta
dawo da kudaden Abacha ya karkatar
Jaridar Cable ta ruwaitp cewa wata majiya
daga fadan shugaban kasa ta ce Sashin
Shari'ah na kasar Amurka (DOJ) ta fadawa
shugaba Buhari yayin da ya ziyarci
Amurka cewa ba su son a tsunduma wasu
mutane cikin batun mayar da kudaden na
Abacha.

Attorney Janar na kasa, Abubakar Malami,
ya yi yunkurin daukan hayar wasu
lauyoyi masu zaman kansu don su taimaka
wajen dawo da kudaden zuwa Najeriya.

Za'a ware wa lauyoyin wani koso cikin
kudin a matsayin la'adan aikinsu duk da
cewa basu taka wata rawa ba wajen
fafutikar gano kudaden da tsohon
shugaban mulkin sojin ya karkatar zuwa
kasashen wajen.

An dai gano kudaden ne a shekarar 2014
karkashin mulkin tsohon shugaban kasa,

Goodluck Ebele Jonathan sannan aka ajiye
kudaden a kasar Amurka. Kazalika, an
biya lauyoyin da sukayi aikin gano kudin
hakkin su na 4% cikin kudin.
Za'a dawo da kudaden ne bayan
gwamnatin tarayya ta sanya hannu a kan
wata yarjejeniya na amincewa ba za'a yi
almubazaranci da kudaden ba kamar
yadda akayi da kudaden da aka dawo wa
Najeriya da su karkashin mulkin Olusegun
Obasanjo.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad