BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MASOYIYATA - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Monday, May 21, 2018

BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MASOYIYATA

Ina fatan aminci da rahmar Ubangijin halitu
su tabbata agareki. Na kasance tamkar mai
jiran 'Gawon shan A kullum cikin jiran
tsammanin ranar da za ki fahimci cewa ni
masoyinki ne na gaskiya Hakika idan har
nace ki sO ni,ki Qi zabin iyayenki na kasance
azzalumin mosoyi soyayya da nake ikirarin
ina yi miki
takasance ta karya. Sam banaso in
kasance mafi son kansa,akan haka nake mai
goyon bayan kar ki aure ni,ki auri zabin
iyayenki kuma ni zan kasance mai taimakinki
akan yiwa
mahaifanki biyayya Ta hakan zan gaskata
soyyata ta gaskiya agareki Koda ace ina da
hanyar da zan bi
domin samun aurenki zan dakatar da kaina
ba don komai ba,sai don dalilan da nake da
su kwara uku.

Dalili na farko banaso in
kasance
masoyin da zai sanya ki baudewa umarnin
iyayenki ko babu komai nasan cewa nima
'yayan da za ki
haifamin watan wata rana zasu baudewa
umarni na Dalilina na biyu kuwa shine mijin
da za ki aura ya dace da ya aure ki dari bisa
dari,ko
ba komai ya baki abinda na ni ban ba ki ba
kuma inaji araina cewar a yadda yake
kaunarki zai kulamin
dake sosai ba wai don ya fini sonki ba
Dalilina na uku kuwa shine idan har ban
kasance mafi son kansa ba,adaidai wannan
ga6a kin fi karfin
aurena Wadannan su ne dalilin da na
dogara da su,don yi wa kaina da ke kanki
adalci. Adalci daya zakiyi
agareni shine komai daran dadewa ki sa
aranki cewa ni ne shugaban
dakarun 'yan amutun sonki,zan cigaba da
sonki ko bayan rabuwarmu kuma da sannun
zan labarta labarinki ga 'yayana in sanar da
su babban rashin da mukayi na
rashinki Ko sau daya ne ki kirani da Jarumin
ki domin samun zafa fan kalaman soyayya
kawai shiganan

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad