Mun samu cewa hukumar zabe ta kasa
watau INEC tare da jam'iyya mai ci ta APC,
sun mayar da martani ga gwamnonin
jam'iyyar adawa ta PDP kan zargin su akan
shirye-shirye da kulla kitimurmura da
aiwatar da magudi yayin zaben 2019.
A yayin mayar da martani hukumar ta
bayyana cewa, 'yan Najeriya sun
aminta da ita wajen tabbatar da gaskiya
gami da adalci yayin gudanar da zaben
a badi, inda a halin yanzu ta ke ci gaba
da kai kawo domin tabbatar da gudanar
zaben cikin inganci da aminci.
Kakakin shugaban hukumar, Mista
Rotimi Oyekanmi, shine ya bayyana
hakan yayin ganawa da manema
labarai cikin babban birnin kasar nan
na tarayya a ranar Litinin din da ta
gabata.
'Yan Najeriya sun aminta da riƙon amanar mu -
INEC ga PDP
Kazalika jam'iyyar ta APC ta mayar da
wannan martani da sanadin kakakin ta
na kasa, Mista Yekini Nabena, yayin
ganawar sa da manema labarai na
jaridar The Punch cikin birnin na Abuja
a ranar da ta gabata.
Mista Nabena ya kuma yi watsi da
ikirarin gwamnonin jam'iyyar ta adawa
kan cewa jam'iyyar APC ta shiga cikin
al'amurra tare da yin kakagida akan
harkokin hukumar INEC domin cimma
manufofin ta.
Jaridar NAIJ.com ta ruwaito cewa,
kungiyar gwamnonin ta jam'iyyar PDP
bisa jagorancin shugabanta gwamnan
jihar Ekiti, Ayodele Fayose, na ci gaba
da zargi gami da tuhumar gwamnatin
tarayya da shugaban kasa Muhammadu
Buhari tare da jam'iyyar sa ta APC kan
kulla kitimurmura ta magudi da kuma
cin karen su ba babbaka yayin zaben
2019.
No comments:
Post a Comment