Dubun wani ‘Dan asalin Najeriya
da ke yaudarar Jama’a a Turai ta
cika
Mun samu labari daga BBC cewa an
kama wani ‘Dan Najeriya da ya hana
Turawa sakat da damfara.
‘Yan Sanda
Kasar Australlia ne su ka cafke wannan
hatsabibin mutumi da ya gagari jama’a.
Wani Mutumin Najeriya ya fitini mutane da 419
a wata kasa
Jami’an tsaron na kasar Australia sun yi
nasarar damke ‘Dan Najeriyar da ke
damfarar mutane ta hanyar aika wasu
sakonni na bogi a shafukan zamani na
gizo.
Wannan mutumin Najeriyar shi ne
shugaban masu wannan danyen aiki na
419.
Yanzu haka dai har wadannan ‘Yan
damfara sun tara makudan kudin da su
ka haura fam Miliyan 3 na Dalar kasar
Australia. Wannan mutumi dai yana yin
wannan aiki ne daga wata cibiyar tsaro
a babban Birnin Sydney na kasar ta
Australia.
KU KARANTA:
Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda na
kasar Arthur Katsogiannis ya bayyana
cewa zai yi wahala a iya gano
wadannan kudi domin tuni har an aika
su Najeriya.
An dai dace wajen cafke
wasu daga cikin masu wannan mugun
aiki a kasar.
Abin mamakin dai shi ne yadda ake
damfarar mutane daga cikin cibiyar
tsaron Hukumar shige-da-fice da ke
Garin Villawood a cikin babban Birnin
Sydney.
Daga cikin wadanda aka kama
har da wasu mata da kuma Matashi mai
shekara 20.
BBC Haussa ta rahoto cewa an yi kira ga
kamfanoni su rika lura da shafukansu
na yanar gizo tare da inganta tsaro da
kuma bi a hankali da kudin shiga. Masu
wannan abu kan labe ne da soyayya
wajen damfara ta hanyar zamba cikin
aminci.
No comments:
Post a Comment