Dalilin Da Yasa Nake Yiwa Mata Waka - Ado Gwanja - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Sunday, September 2, 2018

Dalilin Da Yasa Nake Yiwa Mata Waka - Ado Gwanja

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?
Gwanja: An haife ni a Unguwar Birged da ke
birnin Kano.

Sai dai asalin mahaifina dan
garin Warawa ne, yayin da mahaifiyata
Shuwa Arab ce daga garin Maiduguri a Jihar
Borno.

Na yi karatun firamare a Makarantar
Babbangiji da ke Karkasara. Sannan na yi
sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa.

Bayan na gama ban ci gaba da karatu ba sai
na rika zuwa kasuwa wurin mahaifina.

Bayan mahifina ya rasu ne sai na shiga
buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo ni
matsayin da nake a yanzu.

Mutane da dama sun san Gwanja a fina-
finan Hausa sai kuma ga shi ka canja sheka
zuwa waka, yaya aka yi hakan ta kasance?
Gwanja: To a gaskiya dama waka na fara,
domin na fi shekara 12 ina yin waka, sai dai
a wancan lokaci ba a san ni ba. A wancan
lokaci nakan rubuta waka tun ba ni da kudin
zuwa situdiyo na buga har na rika zuwa ina
bugawa.

Ko ta yi dadi ko ba ta yi ba ban
damu ba, ni dai na san ina waka. To bayan
wani lokaci kuma sai na shiga harkar fim.

Yawancin lokuta an fi ganin kana fitowa a
matsayin dan Daudu a fina-finan Hausa,
haka ka fi mika akalar wakokinka a kan
mata, me ya jawo haka?
Gwanja: To batun fina-finai da nake yi a dan
Daudu wannan yanayin labari ne ya zo da
haka, kasancewar na yi abin da ake bukata a
wasu fina-finai da aka ba ni wannan matsayi
to sai ya zama cewar in dai labari ya zo da
hakan sai a nemo ni a ba ni. Amma ba ni
nake zabe ba.


Shi kuma batun waka da ake ganin na fi yi
wa mata, zan iya cewa saboda su ne iyayen
biki.


Bahushe ya ce inda baki ya karkata ta nan
yawu kan zuba. Kowa ya san irin rawar da
mata ke takawa idan aka zo harkar biki, kin
ga kuwa tunda ina yin wakokin biki, to dole
da su za a yi.


Baya ga wakokin fina-finai da kake yi da na
biki kana yin wakikin siyasa?
Gwanja: Eh ina yin wakoki ga ’yan siaysa,
idan dan siyasar da kansa ya nemi hakan.

Abin da ba na yi shi ne ba na yin waka in kai
wa dan siyasa, saboda na san halinsu sai a
hankali.

Yaya dangantakarka da sauran mawaka?
Gwanja: Gaskiya akwai alaka mai kyau a
tsakaninmu, don akwai girmamamawa a
tsakninmu.
Ba ma yi wa juna hassada ko bakin ciki.

Wane ne gwaninka a fagen wakoki?
Gwanja: Ba ni da gwanin da ya wuce Aminu
Maidawayya.


Kasancewar an fi daukarka don yin wasa a
bukukuwan aure, mutane na zargin cewa ba
ka zuwa biki ko amsa gayyatar talakawa,
mece ce gaskiyar wannan batu?
Gwanja: Gaskiya abin ba haka yake ba. Ai
abin ba kudi ba ne, domin wani ma za ka iya
yi masa kyauta ya danganta da yanayin
mu’amalarku.

Ina ganin duk mutumin da ya zo ku yi
mu’amala ya mutunta ka, domin a da bai zo
wurinka ba. Haka kuma wata rana ba zai zo
wurin naka ba. Kawai ni abin da na sani shi
ne ba a fin karfin masoyi.

Masu yin wadannan kalaman suna yi ne don
ba a yi musu kyauta-kyauta ba ko kuma ma
kai-tsaye in ce kyauta. Kowace sana’a
sunanta sana’a dole mutum ya yi hakuri ya
bi yaddda tsarin abu yake wajen.
Wane tallafi mawaka ke samu daga
gwamnati?
Gwanja: Ni zan iya cewa tsawon rayuwarta a
wannan fage ban taba jin labarin gwamnati
ta ba mu tallafi ko wani abu makamancin
haka ba. Idan ka ga gwamnati ta waiwaye
mu, to so take ta yi amfani da mu don
cimma wata bukatarta ko kuma idan ana
neaman mu biya haraji.

Gwamnati ba ta kallonmu a matsayin
wadanda suka rage mata nauyin neman aiki,
domin akalla ban da nauyin kanmu da muke
dauka muna da yara da ke aiki a
karkashinmu wadanda ta nan suke samun
abin da suke kula da iyalansu.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad