Al Sheikh Malam Ibrahim Nakaka ya zamo
sabon shugaban majalisar Malamai da
Limamai na jahar Kaduna, kamar yadda
jaridar Daily Trust ta samu rahoto daga
jahar Kaduna.
Nakaka ya dare wannan kujerar ne
bayan mutuwar shugaban majalisar,
Sheikh Usman Abubakar Babantune
wanda ya rasu a ranar 10 ga watan
Satumbar 2018 a babban asibitin
koyawar na jami’ar Ahmadu Bello dake
Shika.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito cikin wata
sanarwa da sakataren majalisar, Malam
Yakubu Yusuf Arrigasiyyu ya fitar a
ranar Alhamis din makon data gabata
yana cewa an zabi Nakaka ne banyan
tattaunawa da yayan majalisar.
Malam Arrigasiyyu ya bayyana cewa
majalisar ta zabi Dakta Muhammad
Aliyu Limamin masallacin Juma’a na
Zaria Lowcost a matsayin mataimakin
shugaba na farko.
Hakazalika sanarwar ta kara da
bayyana sunayen Limaman Masallatan
Juma’a na Yahaya road Muhammad
Hassan da na babban masallacin Juma’a
na garin Kafanchan Muhammad Kabir
Qasim a matsayin mataimakan
shuwagabanni na biyu da na uku.
Daga karshen sanarwar, Arrigasiyyu
yayi kira ga yayan majalisar dasu
jajirce tare da hada hannu wajen
gudanar da aiki tukuru wajen ciyar da
addinin Musulunci gaba a Najeriya.
No comments:
Post a Comment