A ranar Talata 24 ga watan Yuli ne
kafatanin Sanatoci suka bayyana rashin
amincwarsu da wani mutumi dan jihar
Legas da wata muhimmiyar bukata da
shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
aiko musu, wanda hakan ya sanya dole
majalisar ta yi watsi da wannan bukata.
NAIJ.com ta ruwaito shugaba Buhari ya
aika ma majalisar da sunan wani jigon
jam’iyyar APC a jihar Legas, Muiz
Banire don su tantance shi kafin ya
nada shi mukamin shugaba hukumar
kwato kadarorin gwamnati, AMCON.
Sai dai da alama Buhari bai bibiyi
Sanatocin ba, wanda hakan ya sanya
dukkanin Sanatoci guda uku da suka
fito daga jihar Legas suka nuna rashin
amincewarsu da wannan mutumi,
sa’annan suka mika ma majalisar
takardar korafi a game da shi.
Muiz Banire
Sanatan Solomon Adeola ne ya fara yin
bore ga wannan bukata ta shugaban
kasa, inda yace: “Akwai korafe korafe
daga mazabata game da nadin Muiz
Banire a matsayin shugaban AMCON,
haka zalika duka Sanatocin jihar Legas
guda uku bamu amince da shi ba.”
A jawabinsa, shugaban majalisar
dattawa, Sanata Bukola Saraki ya
umarci Sanatocin da su aika korafe
korafensu zuwa kwamitin ladabtarwa
ta majalisar dattawa don dubawa.
A ranar 18 ga watan Yuli ne majalisar
ta amshi bukatar da Buhari ya aiko
mata na tantance Banire, inda daga
bisani kwamitin majalisar dake kula da
harkokin kudi ta tantance shi, amma ga
shi yanzu yana fama da kalubale.
No comments:
Post a Comment