Chakwakiyar aure: Idan mijina ya doke ni, ramawa nake yi – Jarumar fim da mijinta ya sabawa kamanni - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Sunday, July 1, 2018

Chakwakiyar aure: Idan mijina ya doke ni, ramawa nake yi – Jarumar fim da mijinta ya sabawa kamanni

Wata jarumar shirin fina-finan kudancin
Najeriya, Bose Omotoyossi, ta bayyana
cewar aurenta da mijinta, dan was an
kwallon kafa, Razaq, ya lalace.

Jim kadan bayan sun yi murnar cika
shekaru 10 da aure, Bose ta bayyana
cewar, mijinta na yawan dukanta hart a
kai gab a zata iya jurewa ba, ita ma ta
fara ramawa.

Saidai a wata hira da tayi da ‘yan
jarida, Bose ta lashe amanta tare da
bayyana cewar aurenta da mijinta na
nan daram.

Bose da mijinta Razaq

“ Na gane cewar nayi kuskuren bayyana
halin da aurenmu ke ciki a dandalin sada
zumunta. Mijina bai taba cewa komai a
kan sabanin da muke samu ba a
dandalin sada zumunta.

“Ranar da muka yi murnar cika shekaru
10 aure ne muka samu wani sabani da
ta kai har mijina ya fasa min waya tare
da yi min duka, hakan ya bani haushi
sosai, domin har yaran mu na kwashe na
bar gidansa domin ya fahimci cewar nayi
fushi sosai ,” a cewar Bose.
Sannan ta kara da cewa, “ muna yawan
samun sabani da mijina, amma yanzu
muna tare kuma muna ziyartar
kwararru domin neman shawarwari da
taimako a kan yadda zamu zauna lafiya
da juna."

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad