Daga cikin jami'an gwamnatin
Najeriyan da ke tare da shi a taron sune
babban lauyan tarayya kuma ministan
shari'a, Abubakar Malami da ministan
harkokin wajen Najeriya, Gepffrey
Onyeama.
Hotuna: Shugaba Buhari a taron gangamin AU a
Mauritania
NAIJ.com ta kawo rahoton cewa
shugaba Muhammadu Buhari, ya isa
birnin birnin Nouakchott, kasar
Mauritania da yammacin nan domin
halartan taron gamayyar kasashen
Afrika wato AU karo na 31 da za’a
gudanar ranan 1 da 2 ga watan Yuli,
2018.
Daga cikin wadanda suka jira saukarshi
a babban filin jirgin saman Nouakchott
sune shugaban kasar Mauritania,
Mohammed Ould Abdel Aziz, da wasu
manyan jami'an gwamnatin kasar.
Hotuna: Shugaba Buhari a taron gangamin AU a
Mauritania
Taron na wannan shekaran dai na ke
take : “Samun nasara kan yaki da
rashawa: Yadda za’a kawo sauyi
nahiyar Afrika”.
Shugaba Muhammadu
Buhari ne zai gabatar da jawabi na
musamman akan wannan take.
Sannan shugaban gamayyar kasashen
Afrikan kuma shugaban kasan
Ruwanda, Paul Kagama, zai gabatar da
jawabi kan sauye-sauyen gamayyar, shi
kuma shugaban kasan Nijar,
Mahamadou Issoufou, zai gabatar da
nasa kan kasuwanci a Afirka.
Hotuna: Shugaba Buhari a taron gangamin AU a
Mauritania
Daga Hausa.naija.ng
No comments:
Post a Comment