Wata mata ta kashe kanta bayan ta gano cewar mijinta ba saurayi bane - Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Your Ad Spot

Thursday, July 19, 2018

Wata mata ta kashe kanta bayan ta gano cewar mijinta ba saurayi bane

Wata ma'aikaciyar jirgin sama, Anissia
Batra, da yanke hunkuncin kashe kanta
bayan ta gano cewa mijinta, Mayank
Singhvi, ya taba auren wata mace daban
kafin ya aureta amma bai sanar da ita ba.

A cewar yan sanda, Batra, wacce ke aiki
tare da wata kamfanin jirgin sama na
kasar Jamus ta shiga cikin bacin rai
sosai tun lokacin data gano mijinta ya
taba aure a kamar yadda Khaleej Times
ta wallafa.

Ta gano cewa Mayank Singhvi ya taba
aure ne misalin wata daya da ya wuce.

Batra da mijinta sunyi auren soyaya na
saurayi da budurwa ne a ranar 23 ga
watan Fabrairun shekarar 2016.

Wata mata ta kashe kanta bayan ta gano cewar
mijinta ba saurayi bane

"Bai sanar da ita ya taba aure a baya ba.
Bayan ta gano cewa yana taba auren,
ranta ya baci sosai.

Ana zargin cewa
sunyi rikici game da batin," inji dan
sandan.

An zargin cewa Anissia ta tayi tsalle ne
daga benen gidanta a ranar Juma'a.

'Yan uwanta sun zargi cewa Mayank
yana dukanta kuma iyayensa suna cin
zarafinta saboda kudin sadaki.

An kama Mayank a ranar Litinin kuma
an gurfanar dashi gaban kotu a ranar
Talata. Kotun kuma ta bayar da
umurnin a tsare shi na kwanaki 14.

"Zamu bukaci a bamu shi bayan mun
gama tattara bayanai daga bakin
shaidu," inji jami'in dan sanda.

Wata kawar Annisia tace yan sanda sun
sanar dasu batun gurfanar da Mayank a
kotu yayin da ake gab da yin jana'izar
marigayiyar.

Hukumar yan sandan tace dan sandan
mai shigar da kara ne ya dace ya sanar
da iyalan wanda suka shigar da kara
game da ranar bayyana a kotun.

'Yan
uwan Annisia kuma sun korafi kan
yadda yan sandan basu kama iyayen
Mayank ba saboda suma suna da hannu
cikin mutuwar ta.

Babban jami'in 'yan sanda, Romil
Baaniya yace an ware iyayen Mayank
daga binciken ne saboda wasu dalilai ba
zai iya bayyanawa ba har sai zuwa
ranar 20 ga watan Yuli. Yace zasu amsa
tambayoyi daga baya.

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad