Arewa Tricks

Hot

Post Top Ad

Post Top Ad

Your Ad Spot

Tuesday, September 18, 2018

mike Ezurounye Jarumin Nollywood ya bada dalilin da yasa ya saka Hadiza Gabon a cikin shirin sa

September 18, 2018 0

Ta shaida cewa ta amince da fitowa cikin
shirin bisa ga ka’ida na cewa baza ta fito a
matsayin da zai sabawa addini ko al’adar ta.

A kwanan baya mun kawo maku labarin
cewa fitacciyar jarumar Kannywood ta fito
a cikin wani shirin fim na turanci wanda
shine na farko da zata yi aiki a
masana'antar fim na Nollywood.

Jaruma mai tauraro ta nuna farin ciki game da
wannan damar na yin fim da wasu jiga-jigan yan
wasan Nollywood.

Ta shaida ma BBChausa cewa ta amince da
fitowa cikin shirin bisa ga ka’ida na cewa baza
ta fito a matsayin da zai sabawa addini ko
al’adar ta.

Tana mai cewa;
“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne
ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna
'Lagos real fake life'
"Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim
dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan
taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da
addini da al'adata ba"
Jarumar ta shaida cewa babu wani bambanci
tsakanin yadda ake yin fina-finai a kannywood
da nollywood face bambancin harshe.

Shahararren jarumi wanda ya shirya shirin yayi
karin haske game da dalilin saka jarumar cikin
shirin duk da cewa bata taba fitowa a cikin wani
shirin Nollywood.

Zantawa da muka yi dashi yayin da ya kawo
mana ziyara, Mike Ezurounye ya nuna
gamsuwar sa yin aiki da ita.

Yayin da yake bada amsar dalilin saka ta a
shirin, jarumin yana mai cewa "Ni mutum ne
wanda ke son saka abun mamaki a cikin fim.

Hadiza tana da basira, ta kware kuma bata taba
yin fim a Nollywood ba"
"Na ware lokaci na musamman domin inyi bincike
akan ayukan ta kuma na tambayi jama'a da dama
game da basirar ta" ya kara.

Mike yace Hadiza ta bada hadin kai dari-bisa
dari kamar yadda ya kamata kuma a bangaren
su sun kiyaye duk wani ka'ida da al'ada da
addininta ya tanadar.

A cewar shi ya ji dadin aiki da ita matuka kuma
akwai wasu aiki biyu da zai so ya kara saka ta
a ciki.

Daga karshe jarumin ya jinjina ma masana'antar
Kannywood, yace kofar shi a bude take wajen
yin aiki da masa'antar.

Shirin 'Lagos real fake life' tana fadarkar da
jama'a game da rayuwar karya da wasu suka sa
a ransu. Manyan fitattun Nijeriya daga
masana'antar fina-finai dake kasar suka fito a
ciki har ma da jaruman kasashen waje.

Za'a fara haska ta ga sinima cikin watan
Nuwamba.

Read More

INEC Hukumar zabe zata haramta amfani da waya wurin zabe

September 18, 2018 0

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya
(INEC) ta haramta zuwa wurin kada kuri'a
da wayar salula.

Shugaban hukumar Farfesa Yakubu Mahmood
ya sanar da haka ranar litinin yayin da ya gana
da jama'a a garin Osogbo gabanin zaben jihar
Osun da za'a gudanar ranar asabar 22 ga watan
Satumba.

A labarin da Channels ta fitar shugaban
hukumar yace an dau matakin ne domin
magance matsalar magudin zabe.
Ya bayyana cewa za'a haramta masu zabe
amfani da waya da zaran an mika masu takardar
kada kuri'a.

Ana zargin cewa masu zabe na daukar hoton
takardar kada kuri'ar su ne domin tabbbatar ma
wakilan jam'iya wanda suka dangwala ma kuri'a.

A cewarsa, za su soma tabbatar da haramcin ne
a zaben da za a yi a jihar Osun da ke kudu
maso yammacin kasar ranar Asabar mai zuwa.
Hakazalika mai magana da yawun hukumar,
Mallam Aliyu Bello, ya tabbatar da wannan
labarin kamar yadda rahoton BBC ya bayyana.
Malam Aliyu ya ce bisa fahimtarsu, masu sayar
da kuri'unsu suna kulla yarjejeniya ta yadda
masu sayar da kuri'a za su nuna wa masu saye
wata shaida da za ta gamsar da su cewa
jam'iyyarsu mutum ya zaba gabanin su biya shi,
don haka wannan dokar za ta magance wannan
matsalar.

Jami'in na hukumar zabe ya yi kira ga 'yan kasar
da su ba su hadin kai wurin ganin sun aiwatar
da dokar ba tare da fuskantar matsaloli ba.

Read More

Sadiq Sani Sadiq da hafsat Idris sune gwarzayen gasar bana

September 18, 2018 0

Ga sunayen jaruman Kannywood da suka lashe
kyautar gasar city people movies Awards na
wannan shekarar.

Kamar yadda aka saba a ko wani shekara,
an gudanar da bikin karrama a fitattun
jarumai da suka taka rawar gani a harkar
nishadi na mujallar City People.

An gudanar da bikin bana a babban wajen taron
biki na Balmoral event center dake jihar Legas
ranar Lahadi 16 ga watan Satumba.

ga wadanda basu sani ba, bikin City People
Movies Awards tana karrama jarumai na
dandalin fim na ko wani masa'anta dake fadin
kasar.

Bana dai a rukunin yan Kannywood Sadiq Sani
Sadiq da Hafsat Idris suka lashe kyautar
gwarazan shekara.

Ga sunayen wadanda suka lashe kyautar gasar
na rukunin hausa daga masana'antar
Kannywood kamar haka:
Sadiq Sani Sadiq - Gwarzon shekara
Hafsat Idris - Gwarzuwar shekara
Abubakar Bashir Maishadda - gwarzon mai
shirya fim
Bello Hafizu - Gwarzon Mai bada umarni
Hannatu Bashir - Mataimakiyar jaruma a cikin
shiri
Asabe Madaki - Ta samu kyautar Sabuwar
jaruma wacce tayi fice
Ahmed Illiyasu Abdulmumin Tan-tiri - Matashin
jarumi na shekara
Ibrahim Sule Katsina da Engr Babagana Abba
Dalori sun samu kyauta ta musamman bisa
gudunmawar da suke badawa a harkar fina-finan
hausa.

Shirin 'Sarauniya'wanda Hassan Giggs ya bada
umarni ya lashe kyautar .

Read More

Monday, September 17, 2018

Sule Lamido ya lissafa ‘yan Najeriya da suka fi Buhari gaskiya da kima

September 17, 2018 0

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa
kuma daya daga cikin masu neman
jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar
shugaban kasa, ya ce Najeriya na cikin
mawuyacin halin rashin lafiya da take
bukatar ‘yan kasa nagari su gaggauta ceto
rayuwarta.
Lamido na wannan kalami ne yau,
Litinin, a Abuja, ga manema labarai
bayan kamala ganawa da wakilan
kungiyoyin kudu da tsakiyar Najeriya.
Kazalika, tsohon gwamnan ya bukaci
‘yan majalisar tarayya da su tsige
Buhari saboda laifukan yiwa kundin
tsarin mulkin kasa karan tsaye.
“ Duk abinda ke faruwa yanzu, na faruwa
ne saboda Najeriya bat a da lafiya.
Najeriya na bukatar shugaba da zai tafi
da duk ‘yan kasa ba tare da nuna
kabilanci ko bangaranci ba ,” a kalaman
Lamido.
Sule Lamido da Buhari
Sannan ya kara da cewa, “ tafiyar da
harkokin gwamnati na fuskantar
barazanar lalacewa a karkashin wannan
gwamnati, shi yasa ake ta aiiyukan
ta’addanci da kashe-kashe a Taraba,
Adamawa, Zamfara da ragowar sassan
Najeriya."

Kazalika, Lamidon ya zargi Buhari da
yunkurin binne irin gudunmawar da
mazan jiya suka bayar wajen gina
Najeriya, mutanen da ya ce Buhari ko
kafar su bai kama ba idan ana maganar
gaskiya da rikon amana.
“ Tun kafin zuwan Buhari akwai mutane
masu kima da gaskiya, akwai Tafawa
Balewa, Obafemi Awolowo, Aminu Kano,
da Azikiwe, wadannan mutane babu
wanda ke tantama a kan rikon amanrsu
da dattako. Ko sau daya Buhari bai taba
yabawa gudunmawar su ba ,” a cewar
Lamido

Read More

2019: Buhari ya gaza amma babu wani da zai iya rikon Najeriya da gaskiya cikin sauran yan takara – Balarabe Musa

September 17, 2018 0

Gabannin zaben 2019, tsohon gwamnan
jihar Kaduna kuma jigon kungiyar
dattawan arewa, Balarabe Musa ya yi duba
sosai ga harkokin kasar sannan ya bayyana
cewa koda dai Shugaban kasa Muhammadu
Buhari ya gazawa ýan Najeriya tun bayan
zabarsa a 2015, babu dan takara ko daya
daga jam’iyyun adawa da ya shirya kai
Najeriya inda take mafarkin kaiwa.

Tsohon gwamnan wanda ya bayyana
hakan a wata hira da manema labarai a
ranar Litinin, 17 ga watan Satumba
yace tulin yan takaran dake neman
shugabanci a yanzu babu wadda ya
nuna cewa zai sanya ci gaba al’umma
sama da son zuciyarsa.

A cewarsa, kasar na bukatar
ingantaccen shugaba a 2019 wadda zai
hada kan kabilun kasar, yayi amfani da
samunta wajen yiwa mutane aiki
sannan ya kawo karshen cin hanci da
rashawa a manyan wurare.
2019: Buhari ya gaza amma babu wani da zai
iya rikon Najeriya da gaskiya cikin sauran yan
takara – Balarabe Musa
Ya kuma koka akan tsarin shiga lamarin
siyasa a kasar, cewa tsadar abun shi ya
hana wadanda ke son kawo ci gaba
fitowa tsanin siyasar kasar.

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa
shugaban majalisar dattawa,

Dr Bukola
Saraki a ranar Litinin, 17 ga watan
Satumba ya bukaci ýan Najeriya da
kada su nuna kabilanci wajen zabar
shugabanni kawai abunda zasu duba
shine hangen nesan shugaba wajen
kawo chanji.

Saraki dan takaarar kujeran shugaban
kasa a jam’iyyar People’s Democratic
Party (PDP) ya bayyana hakan a Lagas
yayinda yake jawabi ga mambobin
jam’iyyar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya
(NAN) ta ruwaito cewa ziyarar da ya kai
sakatarioyar jam’iyyar na daga cikin
rangajin da yake na neman goyon baya
akan kudirinsa.

Read More

Abubuwa 5 da baku sani ba game da Ado Gwanja

September 17, 2018 0

Kusan a iya cewa dukkan masu sha'awar
harkokin fina-finan Hausa musamman ma
mata sun san fitaccen mawakin nan watau
Ado Gwanja.

Shi dai Ado Gwanja a baya an fi ganin
sa ne a cikin fina-finai a matsayin dan
daudu amma kwatsam sai tauraruwar
sa ta soma haskawa a fagen wakoki
musamman ma na biki.

Dandalin Kannywood: Abubuwa 5 da baku sani
ba game da Ado Gwanja

Ga dai wasu daga cikin muhimman
abubuwan da watakila baku sani ba
game da jarumin, kuma mawaki:

1. Ana yi masa lakani da Limamin mata

2. Shi ruwa biyu ne, ma'ana; mahaifin
sa bahaushe ne dan asalin Kano ne,
mahaifiyar sa kuma Shuwa Arab ce 'yar
asalin garin Maiduguri.

3. Waka ya fara kafin shiga harkar fim
domin kuwa ya shafe shekaru akalla 12
yana yin waka amma ba'a san shi ba.

4. Yana da uban gida a harkar wata.
Aminu Mai Dawayya shine uban gidan
sa.

5. Yana yin wakar siyasa idan ya samu
ba na biki kawai yake yi ba.

Read More

Labari cikin hotuna Jarumai Di'ja da Rahama Sadau sun hadu a garin Kaduna

September 17, 2018 0

Rahama ta wallafa hotunan su tare a wajen
taron inda Di'ja ta rungume ta tare da nuna
farin cikin ta bisa ga haduwar su.

Shahararriyar mawakiya Hadiza Blell wanda
aka fi sani da sunan Di'ja ta kai ziyara
mahaifar ta Kaduna inda ta hadu da
abokiyar ta na masana'antar fim.

Mawakiyar Mavins records wanda Don jazzy ke
jagoranta ta gana da masoyan ta dake garin
Kaduna.

Ita ma jarumar fim Rahama Sadau ta ziyarci
wajen taron haduwar domin mara ma abokiyar
aikin ta baya.

Rahama ta wallafa hotunan su tare a wajen
taron inda Di'ja ta rungume ta tare da nuna farin
cikin ta bisa ga haduwar su.

Read More

Gani ya kori ji :- An kama dan majalisa tsirara yana wanka a kasuwa cikin tsakar dare

September 17, 2018 0

Dan majalisar mai suna Timothy Owoeye shine
shugaban jam'iyar mafi rinjaye a majalisar
dokokin jihar Osun.

Dubun wani dan majalisar jihar ta cika
yayin da yaci karo da fusatattun matasa a
daidai inda yake wanka a kasuwa tsakar
dare.

A labarin da Laila News ta fitar dan majalisar
mai suna Timothy Owoeye shine shugaban
jam'iyar mafi rinjaye a majalisar dokokin jihar
Osun.

Jami'an tsaro na kasuwar Osunjela dake garin
Oshogbo suka kama dan majalisar yayin da suke
sintiri .

Dan majalisar yana wakiltar yankin Ilesa ta
gabas a majalisar dokokin jiha karkashin jam'iya
mai mulki ta APC.

Yayin da harkar siyasa ya kara kamari bisa ga
matsowar zaben 2019, wasu daga cikin
abubuwa da wannan lokacin ke haifarwa shine
labarin tsubbu da asiri.

Read More

Post Top Ad