Tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas dake a
kudu maso kudancin Najeriya na farko a
wannan jamhuriyar,
Mista Donald Duke a
ranar Alhamis din da ta gabata ya yi
ikirarin cewa asarar da Najeriya ta tafka
sakamakon fadan Boko Haram ya fi wadda
ta yi a lokacin yakin basasa.
Mista Duke dai ya yi wannan ikirarin
ne a yayin zantawa da manema labarai
a garin Legas,
karkashin inuwar wata
kungiya da ke rajin tabbatar da shugaba
mai inganci a Najeriya watau National
Movement for Positive Change (NMPC).
Yadda wasu 'yan Najeriya ke kasuwanci da
fadan Boko Haram - Tsohon Gwamna
Haka zalika tsohon gwamnan kuma ya
kara fallasa cewa rikicin na Boko
Haram ko shakka babu ya mayar da
wasu hamshakan masu kudi inda suka
mayar da abun tamkar wata sabuwar
kasuwa da ta bude kamar dai yadda
muka samu daga majiyar mu.
A wani labarin kuma, Tsohon gwamnan
jihar Sokoto na farko a wannan
jamhuriyar kuma jigo a jam'iyyar PDP a
jihar yanzu haka watau Alhaji Attahiru
Bafarawa ya yi ikirarin cewa tsaffin
gwamnonin nan na jam'iyyar PDP da
suka sauya sheka ya zuwa APC a
shekarar 2014 sun baiwa sabuwar
jam'iyyar ta su kudin kamfen na Naira
miliyan 500.
A cewar sa, kafin jam'iyyar ta APC ta
amince da dawowar su tare kuma da
mallaka masu ragamar jam'iyyar
jihohin nasu a hannun su sai da aka
umurce su da kowa ya bayar da Naira
miliyan 100.
No comments:
Post a Comment