Kungiyar ta bayyana dalilain da ya sanya zasu
nada jarumin da sarautar bayan tattaunawa da
suka yi tsakanin su
Kungiyar masu kallon fina-finan hausa na
shirin nada jarumi Adam A. Zango da
sarautar sarkin kannywood bisa
gwagwarmayar da yake a masana'antar
nishadantarwa.
Falla M Sherrif wanda yake shine shugaba mai
riko na kungiyar ya zanta wa jaridar RARIYA
cewa kungiyar zata nada jarumin da sarautar
bayan tattaunawa da tayi kan wanda yafi
cancanta.
Ya bayyana dalilai da yasa zasu ba Adam Zango
sarauta kamar haka : "Don kasancewar sa mai
hakuri, iliminsa mutuncinsa, kyautarsa, biyayyarsa,
ibadarsa, yafiyarsa ida an yi masa laifi da kuma
daukakarsa. Sannan kuma mawaki ne, makadi
ne,furodusa ne, darakta ne, edita ne, jarumi ne,
dan rawa ne da dai sauransu.
Shugaban kungiyar ya kuma kara da cewa, yanci
da masu kallo ke dashi a wajen masu shirya
fina-finai yana daga cikin dalilin nada shi
saboda a dalilin su ake shirye fina-finan hausa
domin su siya.
Al'amarin ya janyo farin cikin ga dinbim
masoyan jarumin 'Gwaska" inda suka gudanar
da biki na taya murnar samun wannan sarauta.
Sai dai wannan sabon sarauta zai raba hankalin
jama'a ya kuma sanya alamar tambaya ga masu
bibiyan masana'antar Kannywood.
Sanin jama'a ne cewa an nada jarumi Ali Nuhu
da wannan sarautar kuma mafi yawanci ma
dashi aka yi masa lakabi.
A wata sako da ya wallafa a shafin sa na
Instagram kwanan baya, jarumi Bello
Muhammed Bello yayi kira na a gudanar da
zabe domin nada sarautar Sarkin kannywood
domin bada hanyar zaben wanda yafi cancanta.
No comments:
Post a Comment