Amfanin Shan Madarar Raƙumi ga Lafiyar
Ɗan-adam
Madarar raƙumi ko nonon raƙumi (camel
milk) sinadari ce mai matukar amfani ga
lafiyar ɗan adam. Tsawon lokaci mai yawa
Larabawa masu yawon kiwo da Buzaye a
cikin sararin sahara sun kasance suna
amfani da wannan madara wacce ake
tatsowa daga hantsar dabbar taguwa a
matsayin abinci abar sha da kuma magani
a cikin tafiyarsu mai nisa cikin sahara
domin rayuwa.
Taguwa dabba ce mai asali da ban mamaki
dake rayuwa musamman a yankunan
sahara masu tsananin zafi a duniya.
Tsawon lokaci mai yawa , tarihi ya nuna
cewa mutanen sahara na amfani da madara
ko fitsarin wannan dabba wajen magance
matsalolin lafiya na daban-daban. Allah
(S.W.A.) Yasa albarka da waraka a cikin
madarar wannan dabba wacce bata da
abinci daya wuce itacen ƙaya da ruwa a
dajin sahara. Itacen ƙaya da wannan dabba
ke ci anyi imani cewa mafi yawansu na
ɗauke da magunguna wanda za'a iya samun
amfaninsu cikin madarar idan mutum ya
sha ta. Bugu da ƙari, ana sarrafa madarar
domin samar da wani abinci dake ake cema
CUKU ko CUKWI (Camel cheese) .Shin ko ka
taba ganin harshen raƙumi a mahauta
bayan an yanka/soke shi? Da yawa zaka ga
ƙaya mai tsawo cikin harshen duk ta soke/
lume cikin tsokar harshen saboda yawan
cin ƙayarsa.
Binciken kimiyya na nuna cewa saboda
muhimmancin madarar raƙumi itace mafi
kusa a cikin nau'in madarar dabbobi dake
da yanayin amfani kusan irin na madarar
ɗan adam, wato madarar da uwa ke bawa
jinjirinta mai roman sinadarai masu yawa
da inganta lafiyarsa. Saboda haka ne da
yawa ake bawa jinjirin mutum madarar
raƙumi wanda baya samun isasshen abinci
mai lafiya a wasu al'adun. Abin nufi anan
shine, madarar raƙumi ta banbanta da
sauran nau'in madarar dabbobi kamar
irinsu sanuwa, tumkiya da akuya
kasancewar ta zarce su amfani a cikin jikin
ɗan adam mai amfani da ita (mai shan
madarar). Madarar rakumi na dauke da
sinadari mai ƙara yawan jini da hana
rashin jinin (iron) mai yawa wanda yafi
yawan wanda ke akwai cikin madarar
sanuwa har linki 10 da kuma sinadari mai
ƙarfafa garkuwar jiki (vitamin c) wanda
shima yafi yawan wanda madarar sanuwa
ke ɗauke dashi sau 3. Madarar raƙumi na
ƙunshe da sinadari mai gina-jiki (protein)
mai yawa tare da wasu sinadarai masu
bayarda da kariya daga cututtuka. Irin
waɗannan sinadarai ana samun su kaɗan
ne cikin madarar sanuwa idan aka
kwatanta da ta raƙumi.
Amfanin madarar raƙumi a taƙaice - wasu
daga cikin manya-manyan amfaninta, sune:
(Health benefits of camel milk)
1. Tana taimakawa masu ciwon-suga
(diabetes). Madarar raƙumi na ƙunshe da
sinadaran inganta lafiya da kuma sinadarin
INSULIN mai yawa . Masu ciwon-suga zasu
more amfaninta ta sosai.
2. Tana taimakawa masu rashin lafiyar
OSTIZAM (AUSTISM), wanda wata matsalar
ƙwalwa ce dake bayyana tun farkon
yarintar mutum wacce ke hana marar
lafiyar yin tarayya mai kyau da mutane -
wato haɗuwa da mutane da yin abokanai
da kuma sanya sa wuyar magana, tunani ko
sadarwa tsananin sa da sauran mutane.
Madarar raƙumi nada wasu sinadarai masu
sanya mararsa lafiyar su sami sauƙi sosai
koma waraka daga wannan rashin lafiyar.
3.Tana taimakawa masu ALAJI (ALLERGY) ,
wato wani yanayi da garkuwar jikin mutum
ke nuna bata son wani abu , musamman
abinda bai cika cutar da lafiya ba ko kuma
baya cutar da mutane da dama amma sai
ya cutar da mutum , yasa garkuwar jikinsa
tayi tutsu bata son abin (allergic reaction).
Misali, kamar wani nau'in abinci da baya
cutar da lafiya amma idan mutum yaci sai
yasa shi rashin lafiya, ko ruwan damuna
kawai ya sanya ƙuraje su fito ma mutum ga
jiki ko ƙaiƙayi, ko warin wata dabba yasa
mutum atishawa ko mura, ko kuma taɓa
wata dabba ko wani abu ya sanya rashin
lafiya da sauransu. Shan madarar raƙumi
na magance dangin waɗannan matsaloli
abisa wasu bincike-bincike da aka gudanar.
4. ƙarfafa garkuwar jiki. Sinadarai masu
ƙarfafa halittun garkuwar jiki dake cikin
madarar raƙumi sun isa suyi yaƙi da
cututtuka masu kai farmaki a cikin jikin
ɗan-adam su halaka cututtukan.
5. Gina jiki da ƙoshin lafiya. Yawan
sinadarai masu gina-jiki (proteins) dake
cikin madarar na taimakawa wajen girman
jiki da cigabansa.
6. Inganta lafiyar zuciya. Madarar nada
sinadarai (FATTY ACIDS) wanda zasu iya
daidaita sinadarin kolestarol
( CHOLESTEROL) dake cikin jini. Yawan
kolestarol a jini nada haɗari, sinadari ne
mai danƙo wanda zai iya toshe ƙofofin jinin
zuciya (fayif) da take harba jini dasu zuwa
sassan jiki (arteries). Idan hakan ya faru
zai iya yin dameji ga zuciya. Madarar zata
iya rage haɗarin faruwar damejin zuciya,
mutuwar sashen jiki da kuma rage hawan
jini , da sauran su.
No comments:
Post a Comment