Hira Mai Ratsa Zuciya Daga Majalisar Annabi (SAW)
Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta
Yace: "Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?
Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_
1: zama a gaban ka,
2: kallon ka,
3: ciyar da dukiya ta gare ka
Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki
Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?
Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_
1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne,
2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,
3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci.
_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_
_Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_
1: ciyar da abinci ga mabukaci,
2: yada sallama,
3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.
_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_
_Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_
1: Azumi a lokacin rani,
2: Karrama bako,
3: yakar abokan gaba da takobbi.
_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_
_Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_
1: yunwa,
2: jinya,
3: mutuwa.
_Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_
Sai Aba zarri yace:
*ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,
*ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi,
*ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na
_A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_
1: isar da sako,
2: bayar da amana,
3: son nakasassu.
_Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah da sahabbai tayi dadi, harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku_
1: harshe mai ambatonSa,
2: zuciya mai tsoronSa,
3: jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri#.
_Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah Girma da tsarki sun tabbata Allah_
Adu'o'i guda uku kada ku manta su acikin sujjadarku..
"Ya Allah ina rokonka kyawawan halaye".
"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace"
"Ya ALLAH mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka"
Lalle wannan ya cancanta ku tura zuwa ga waninku domin ya amfana.
Dauki darasin ka a cikin wannan hadisi, ka aikata shi, za ka yi nasara.
Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne, yi kokari ka fita a sahun farko na daliban makarantar.
No comments:
Post a Comment